caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Ash-Sharh الشرح

Ayoyi 8 · Makka · tsarin saukarwa 12

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَوَضَعْنَا عَنكَ وِزْرَكَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِىٓ أَنقَضَ ظَهْرَكَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda ya nauyayi bãyanka?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِنَّ مَعَ ٱلْعُسْرِ يُسْرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ مَعَ ٱلْعُسْرِ يُسْرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا فَرَغْتَ فَٱنصَبْ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرْغَب

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70