Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ãyõyi bayyanannu a cikinta, dõmin ku riƙa tunãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMazinãciya da mazinãci,[1] to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMazinãci bã ya aure[1] fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda ke jĩfar[1] mãtã masu kãmun kai, sa'an nan kuma ba su jẽ da shaidu huɗu ba to, ku yi musu bũlãla, bũlãla tamãnin, kuma kada ku karɓi wata shaida tãsu, har abada. Waɗancan su ne fãsiƙai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda ke jĩfar mãtan[1] aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga magasganta.'
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne waɗanda[1] suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDon me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?"
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDon me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne, dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma"?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kada[1] ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne waɗannan da suke jĩfar mãtã mãsu kãmun kai gãfilai[1] mũminai, an la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma sunãda azãba mai girma.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMiyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun[1] maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da (mãsu ƙazafi) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama[1] a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan ba ku sãmi kõwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku izni. Kuma idan an ce muku, "Ku kõma." Sai ku kõma, shi ne mafi tsarkaka a gare ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBãbu laifi a kanku, ga ku shiga gidãje waɗanda bã zaunannu ba, a cikinsu akwai waɗansu kãya nãku. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke nũnãwa, da abin dakuke ɓãyẽwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjõjinsu.[1] wannan shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã'antãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan[1] ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu,[1] dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ãyõyi mãsu bayyanãwa, da misãli daga waɗanda suka shige daga gabãninku, da wa'azi ga mãsu taƙawa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAllah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a cikinsu, sãfe da maraice.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗansu maza, waɗanda wani fatauci bã ya shagaltar da su, kuma sayarwa bã ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bãyar da zakka, sunã tsõron wani yini wanda zukãta sunã bibbirkita a cikinsa, da gannai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙãra musu daga falalarsa. Kuma Allah Yanã azurta wanda Yake so, bã da lissafi ba.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi[1] Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKõ kuwa kamar[1] duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa sunã yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sunã mãsu sanwa, kõwane lalle ya san sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yanã kõra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a tsakãninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yanã fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwãtsu a cikinsa na ƙanƙarã daga sama, sai ya sãmu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yanã kusa ya tafi da gannai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafãfu biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yãna halitta abin da Yake so, lalle Allah, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne haƙĩƙa Mun saukar da ãyõyi, mãsu bayyanãwa. Kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sunã cẽwa, "Mun yi ĩmãni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗã'ã." Sa'an nan kuma wata ƙungiya daga gare su, su jũya daga bãyan wancan. Kuma waɗancan ba mũminai ba ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan aka kirã su zuwa ga Allah da ManzonSa, dõmin Ya yi hukunci[1] a tsakãninsu, sai gã wata ƙnngiya daga gare su sunã mãsu bijirewa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, a cikin zukãtansu akwai cũta ne, ko kuwa sunã tsõron Allah Ya yi zãlunci a kansu da ManzonSa? Ã'a, waɗancan sũ ne azzãlumai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMaganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da Manzon Sa dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu takan kasance kawai su ce "Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wanda ya yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsõron Allah, ya kuma bĩ Shi da taƙawa to waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa sunã fita.' Ka ce, "Kada ku rantse, ɗã'ã sananna ce! Lalle ne, Allah Mai ƙididdigewã ne ga abin da kuke aikatãwã."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan Manzo fãce iyarwa bayyananna."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAllah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKada lalle ka yi zaton waɗanda suka kãfirta zã su buwãya a cikin ƙasa, kuma makõmarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar tã mũnana.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni[1] sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyin Sa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan yãra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda waɗanda suke a gabãninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyin Sa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma tsõfaffi daga mãtã, waɗanda bã su fatan wani aure to, bãbu laifi a kansu su ajiye tufãfinsu, bã sunã mãsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku,[1] gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai[1].
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKada ku sanya kiran Manzo[1] a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke sãɓãwa daga umurnin Sa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba mai raɗãɗi ta sãme su.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa, Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme, Masani ne.