Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutãne misãlansu.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah,[1] to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani).
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa, zai zama kamar wanda aka ƙawãce masa mugun aikinsa, kuma suka bibbiyi son zũciyõyinsu?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMisãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare[1] zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi "Mẽne ne (Muhammadu) ya fãɗa ɗazu?" Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son zũciyõyinsu.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo shin sunã jiran (wani abu)? Fãce Sa'a ta jẽ musu bisa abku. dõmin lalle sharuɗɗanta sun zo. To, yãya tunãwarsu[1] take, idan har ta jẽ musu?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka,[1] (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? "To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu,[1] to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su.
Hausa Translation - Abu Bakr Jumilalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta [1]musu (haka), kuma ya yi musu shibta.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin," alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã sanin ayyukanku.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka saɓa wa Manzon sa a bãyan shiriyar ta bayyana a gare su, bã za su cũci Allah da kõme ba, kuma zã Ya ɓãta ayyukansu.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara ba a gare su.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai[1] ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDã Allah zai tambaye ku su (dũkiyõyin) har Ya wajabta muku bãyarwa, zã ku yi rõwa kuma Ya fitar da miyãgun ƙulle-ƙullenku.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya (daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su kasance kwatankwacinku ba.