caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Humaza الهمزة

Ayoyi 9 · Makka · tsarin saukarwa 32

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَيْلٌ لِّكُلِّ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِى جَمَعَ مَالًا وَعَدَّدَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخْلَدَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّا لَيُنۢبَذَنَّ فِى ٱلْحُطَمَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْحُطَمَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

نَارُ ٱللَّهِ ٱلْمُوقَدَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWutar Allah ce wadda ake hurawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّتِى تَطَّلِعُ عَلَى ٱلْأَفْـِٔدَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWadda take lẽƙãwa a kan zukata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّهَا عَلَيْهِم مُّؤْصَدَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فِى عَمَدٍ مُّمَدَّدَةٍۭ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70