caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Qasas القصص

Ayoyi 88 · Makka · tsarin saukarwa 49

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ طسٓمٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiT. S̃. M̃.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تِلْكَ ءَايَٰتُ ٱلْكِتَٰبِ ٱلْمُبِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

نَتْلُوا۟ عَلَيْكَ مِن نَّبَإِ مُوسَىٰ وَفِرْعَوْنَ بِٱلْحَقِّ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMunã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ فِرْعَوْنَ عَلَا فِى ٱلْأَرْضِ وَجَعَلَ أَهْلَهَا شِيَعًا يَسْتَضْعِفُ طَآئِفَةً مِّنْهُمْ يُذَبِّحُ أَبْنَآءَهُمْ وَيَسْتَحْىِۦ نِسَآءَهُمْ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلْمُفْسِدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱسْتُضْعِفُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَنَجْعَلَهُمْ أَئِمَّةً وَنَجْعَلَهُمُ ٱلْوَٰرِثِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنُمَكِّنَ لَهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَنُرِىَ فِرْعَوْنَ وَهَٰمَٰنَ وَجُنُودَهُمَا مِنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَحْذَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰٓ أُمِّ مُوسَىٰٓ أَنْ أَرْضِعِيهِ فَإِذَا خِفْتِ عَلَيْهِ فَأَلْقِيهِ فِى ٱلْيَمِّ وَلَا تَخَافِى وَلَا تَحْزَنِىٓ إِنَّا رَآدُّوهُ إِلَيْكِ وَجَاعِلُوهُ مِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلْتَقَطَهُۥٓ ءَالُ فِرْعَوْنَ لِيَكُونَ لَهُمْ عَدُوًّا وَحَزَنًا إِنَّ فِرْعَوْنَ وَهَٰمَٰنَ وَجُنُودَهُمَا كَانُوا۟ خَٰطِـِٔينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَتِ ٱمْرَأَتُ فِرْعَوْنَ قُرَّتُ عَيْنٍ لِّى وَلَكَ لَا تَقْتُلُوهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوْ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدًا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma matar[1] Fir'auna ta ce ("Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã," alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَصْبَحَ فُؤَادُ أُمِّ مُوسَىٰ فَٰرِغًا إِن كَادَتْ لَتُبْدِى بِهِۦ لَوْلَآ أَن رَّبَطْنَا عَلَىٰ قَلْبِهَا لِتَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta.[1] Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَتْ لِأُخْتِهِۦ قُصِّيهِ فَبَصُرَتْ بِهِۦ عَن جُنُبٍ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ta ce wa 'yar'uwarsa,[1] "Ki bĩ shi." Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَحَرَّمْنَا عَلَيْهِ ٱلْمَرَاضِعَ مِن قَبْلُ فَقَالَتْ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَىٰٓ أَهْلِ بَيْتٍ يَكْفُلُونَهُۥ لَكُمْ وَهُمْ لَهُۥ نَٰصِحُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: "Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَرَدَدْنَٰهُ إِلَىٰٓ أُمِّهِۦ كَىْ تَقَرَّ عَيْنُهَا وَلَا تَحْزَنَ وَلِتَعْلَمَ أَنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسْتَوَىٰٓ ءَاتَيْنَٰهُ حُكْمًا وَعِلْمًا وَكَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci[1] da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَدَخَلَ ٱلْمَدِينَةَ عَلَىٰ حِينِ غَفْلَةٍ مِّنْ أَهْلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيْنِ يَقْتَتِلَانِ هَٰذَا مِن شِيعَتِهِۦ وَهَٰذَا مِنْ عَدُوِّهِۦ فَٱسْتَغَٰثَهُ ٱلَّذِى مِن شِيعَتِهِۦ عَلَى ٱلَّذِى مِنْ عَدُوِّهِۦ فَوَكَزَهُۥ مُوسَىٰ فَقَضَىٰ عَلَيْهِ قَالَ هَٰذَا مِنْ عَمَلِ ٱلشَّيْطَٰنِ إِنَّهُۥ عَدُوٌّ مُّضِلٌّ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ رَبِّ إِنِّى ظَلَمْتُ نَفْسِى فَٱغْفِرْ لِى فَغَفَرَ لَهُۥٓ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara." Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ رَبِّ بِمَآ أَنْعَمْتَ عَلَىَّ فَلَنْ أَكُونَ ظَهِيرًا لِّلْمُجْرِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni'imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَصْبَحَ فِى ٱلْمَدِينَةِ خَآئِفًا يَتَرَقَّبُ فَإِذَا ٱلَّذِى ٱسْتَنصَرَهُۥ بِٱلْأَمْسِ يَسْتَصْرِخُهُۥ قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰٓ إِنَّكَ لَغَوِىٌّ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, "Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّآ أَنْ أَرَادَ أَن يَبْطِشَ بِٱلَّذِى هُوَ عَدُوٌّ لَّهُمَا قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ أَتُرِيدُ أَن تَقْتُلَنِى كَمَا قَتَلْتَ نَفْسًۢا بِٱلْأَمْسِ إِن تُرِيدُ إِلَّآ أَن تَكُونَ جَبَّارًا فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا تُرِيدُ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلْمُصْلِحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce,[1] "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa[2] a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَآءَ رَجُلٌ مِّنْ أَقْصَا ٱلْمَدِينَةِ يَسْعَىٰ قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ إِنَّ ٱلْمَلَأَ يَأْتَمِرُونَ بِكَ لِيَقْتُلُوكَ فَٱخْرُجْ إِنِّى لَكَ مِنَ ٱلنَّٰصِحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: "Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَخَرَجَ مِنْهَا خَآئِفًا يَتَرَقَّبُ قَالَ رَبِّ نَجِّنِى مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّٰلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya fita daga gare ta,[1] yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَمَّا تَوَجَّهَ تِلْقَآءَ مَدْيَنَ قَالَ عَسَىٰ رَبِّىٓ أَن يَهْدِيَنِى سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: "Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدْيَنَ وَجَدَ عَلَيْهِ أُمَّةً مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسْقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمْرَأَتَيْنِ تَذُودَانِ قَالَ مَا خَطْبُكُمَا قَالَتَا لَا نَسْقِى حَتَّىٰ يُصْدِرَ ٱلرِّعَآءُ وَأَبُونَا شَيْخٌ كَبِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho[1] ne mai daraja."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَسَقَىٰ لَهُمَا ثُمَّ تَوَلَّىٰٓ إِلَى ٱلظِّلِّ فَقَالَ رَبِّ إِنِّى لِمَآ أَنزَلْتَ إِلَىَّ مِنْ خَيْرٍ فَقِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَجَآءَتْهُ إِحْدَىٰهُمَا تَمْشِى عَلَى ٱسْتِحْيَآءٍ قَالَتْ إِنَّ أَبِى يَدْعُوكَ لِيَجْزِيَكَ أَجْرَ مَا سَقَيْتَ لَنَا فَلَمَّا جَآءَهُۥ وَقَصَّ عَلَيْهِ ٱلْقَصَصَ قَالَ لَا تَخَفْ نَجَوْتَ مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّٰلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu." To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: "Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَتْ إِحْدَىٰهُمَا يَٰٓأَبَتِ ٱسْتَـْٔجِرْهُ إِنَّ خَيْرَ مَنِ ٱسْتَـْٔجَرْتَ ٱلْقَوِىُّ ٱلْأَمِينُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi¦ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi[1] amintacce."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ إِنِّىٓ أُرِيدُ أَنْ أُنكِحَكَ إِحْدَى ٱبْنَتَىَّ هَٰتَيْنِ عَلَىٰٓ أَن تَأْجُرَنِى ثَمَٰنِىَ حِجَجٍ فَإِنْ أَتْمَمْتَ عَشْرًا فَمِنْ عِندِكَ وَمَآ أُرِيدُ أَنْ أَشُقَّ عَلَيْكَ سَتَجِدُنِىٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ ذَٰلِكَ بَيْنِى وَبَيْنَكَ أَيَّمَا ٱلْأَجَلَيْنِ قَضَيْتُ فَلَا عُدْوَٰنَ عَلَىَّ وَٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّا قَضَىٰ مُوسَى ٱلْأَجَلَ وَسَارَ بِأَهْلِهِۦٓ ءَانَسَ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ نَارًا قَالَ لِأَهْلِهِ ٱمْكُثُوٓا۟ إِنِّىٓ ءَانَسْتُ نَارًا لَّعَلِّىٓ ءَاتِيكُم مِّنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ جَذْوَةٍ مِّنَ ٱلنَّارِ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, "Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِىَ مِن شَٰطِئِ ٱلْوَادِ ٱلْأَيْمَنِ فِى ٱلْبُقْعَةِ ٱلْمُبَٰرَكَةِ مِنَ ٱلشَّجَرَةِ أَن يَٰمُوسَىٰٓ إِنِّىٓ أَنَا ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَٰلَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) "Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنٌّ وَلَّىٰ مُدْبِرًا وَلَمْ يُعَقِّبْ يَٰمُوسَىٰٓ أَقْبِلْ وَلَا تَخَفْ إِنَّكَ مِنَ ٱلْـَٔامِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. "Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱسْلُكْ يَدَكَ فِى جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَآءَ مِنْ غَيْرِ سُوٓءٍ وَٱضْمُمْ إِلَيْكَ جَنَاحَكَ مِنَ ٱلرَّهْبِ فَذَٰنِكَ بُرْهَٰنَانِ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦٓ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمًا فَٰسِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ رَبِّ إِنِّى قَتَلْتُ مِنْهُمْ نَفْسًا فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَخِى هَٰرُونُ هُوَ أَفْصَحُ مِنِّى لِسَانًا فَأَرْسِلْهُ مَعِىَ رِدْءًا يُصَدِّقُنِىٓ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ɗan'uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ سَنَشُدُّ عَضُدَكَ بِأَخِيكَ وَنَجْعَلُ لَكُمَا سُلْطَٰنًا فَلَا يَصِلُونَ إِلَيْكُمَا بِـَٔايَٰتِنَآ أَنتُمَا وَمَنِ ٱتَّبَعَكُمَا ٱلْغَٰلِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّا جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا بَيِّنَٰتٍ قَالُوا۟ مَا هَٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ مُّفْتَرًى وَمَا سَمِعْنَا بِهَٰذَا فِىٓ ءَابَآئِنَا ٱلْأَوَّلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّىٓ أَعْلَمُ بِمَن جَآءَ بِٱلْهُدَىٰ مِنْ عِندِهِۦ وَمَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِ إِنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلظَّٰلِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَأُ مَا عَلِمْتُ لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرِى فَأَوْقِدْ لِى يَٰهَٰمَٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجْعَل لِّى صَرْحًا لَّعَلِّىٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّى لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلْكَٰذِبِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka[1] (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱسْتَكْبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُۥ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُمْ إِلَيْنَا لَا يُرْجَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَخَذْنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذْنَٰهُمْ فِى ٱلْيَمِّ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلظَّٰلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَٰهُمْ أَئِمَّةً يَدْعُونَ إِلَى ٱلنَّارِ وَيَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ لَا يُنصَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَتْبَعْنَٰهُمْ فِى هَٰذِهِ ٱلدُّنْيَا لَعْنَةً وَيَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ هُم مِّنَ ٱلْمَقْبُوحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَٰبَ مِنۢ بَعْدِ مَآ أَهْلَكْنَا ٱلْقُرُونَ ٱلْأُولَىٰ بَصَآئِرَ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةً لَّعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلْغَرْبِىِّ إِذْ قَضَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَى ٱلْأَمْرَ وَمَا كُنتَ مِنَ ٱلشَّٰهِدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَٰكِنَّآ أَنشَأْنَا قُرُونًا فَتَطَاوَلَ عَلَيْهِمُ ٱلْعُمُرُ وَمَا كُنتَ ثَاوِيًا فِىٓ أَهْلِ مَدْيَنَ تَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَٰتِنَا وَلَٰكِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game[1] da waɗancan lãbarai).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلطُّورِ إِذْ نَادَيْنَا وَلَٰكِن رَّحْمَةً مِّن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّآ أَتَىٰهُم مِّن نَّذِيرٍ مِّن قَبْلِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْلَآ أَن تُصِيبَهُم مُّصِيبَةٌۢ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَيَقُولُوا۟ رَبَّنَا لَوْلَآ أَرْسَلْتَ إِلَيْنَا رَسُولًا فَنَتَّبِعَ ءَايَٰتِكَ وَنَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: "Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa, kuma mu kasance daga mũminai?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُوا۟ لَوْلَآ أُوتِىَ مِثْلَ مَآ أُوتِىَ مُوسَىٰٓ أَوَلَمْ يَكْفُرُوا۟ بِمَآ أُوتِىَ مُوسَىٰ مِن قَبْلُ قَالُوا۟ سِحْرَانِ تَظَٰهَرَا وَقَالُوٓا۟ إِنَّا بِكُلٍّ كَٰفِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurin Mu, suka ce: "Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: "Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna," kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ فَأْتُوا۟ بِكِتَٰبٍ مِّنْ عِندِ ٱللَّهِ هُوَ أَهْدَىٰ مِنْهُمَآ أَتَّبِعْهُ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِن لَّمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَكَ فَٱعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَآءَهُمْ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيْرِ هُدًى مِّنَ ٱللَّهِ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّٰلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ وَصَّلْنَا لَهُمُ ٱلْقَوْلَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar[1] da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَٰهُمُ ٱلْكِتَٰبَ مِن قَبْلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa (Alƙur'ãni), su mãsu ĩmãni ne da shi.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلِهِۦ مُسْلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: "Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أُو۟لَٰٓئِكَ يُؤْتَوْنَ أَجْرَهُم مَّرَّتَيْنِ بِمَا صَبَرُوا۟ وَيَدْرَءُونَ بِٱلْحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقْنَٰهُمْ يُنفِقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗancan anã ba su lãdansu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا سَمِعُوا۟ ٱللَّغْوَ أَعْرَضُوا۟ عَنْهُ وَقَالُوا۟ لَنَآ أَعْمَٰلُنَا وَلَكُمْ أَعْمَٰلُكُمْ سَلَٰمٌ عَلَيْكُمْ لَا نَبْتَغِى ٱلْجَٰهِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma)."[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّكَ لَا تَهْدِى مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهْدِى مَن يَشَآءُ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne kai bã ka shiryar[1] da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالُوٓا۟ إِن نَّتَّبِعِ ٱلْهُدَىٰ مَعَكَ نُتَخَطَّفْ مِنْ أَرْضِنَآ أَوَلَمْ نُمَكِّن لَّهُمْ حَرَمًا ءَامِنًا يُجْبَىٰٓ إِلَيْهِ ثَمَرَٰتُ كُلِّ شَىْءٍ رِّزْقًا مِّن لَّدُنَّا وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu[1] daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍۭ بَطِرَتْ مَعِيشَتَهَا فَتِلْكَ مَسَٰكِنُهُمْ لَمْ تُسْكَن مِّنۢ بَعْدِهِمْ إِلَّا قَلِيلًا وَكُنَّا نَحْنُ ٱلْوَٰرِثِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا كَانَ رَبُّكَ مُهْلِكَ ٱلْقُرَىٰ حَتَّىٰ يَبْعَثَ فِىٓ أُمِّهَا رَسُولًا يَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَٰتِنَا وَمَا كُنَّا مُهْلِكِى ٱلْقُرَىٰٓ إِلَّا وَأَهْلُهَا ظَٰلِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَىْءٍ فَمَتَٰعُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَزِينَتُهَا وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰٓ أَفَلَا تَعْقِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَمَن وَعَدْنَٰهُ وَعْدًا حَسَنًا فَهُوَ لَٰقِيهِ كَمَن مَّتَّعْنَٰهُ مَتَٰعَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ثُمَّ هُوَ يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ مِنَ ٱلْمُحْضَرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã rayãwa?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيْهِمُ ٱلْقَوْلُ رَبَّنَا هَٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَغْوَيْنَآ أَغْوَيْنَٰهُمْ كَمَا غَوَيْنَا تَبَرَّأْنَآ إِلَيْكَ مَا كَانُوٓا۟ إِيَّانَا يَعْبُدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقِيلَ ٱدْعُوا۟ شُرَكَآءَكُمْ فَدَعَوْهُمْ فَلَمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَهُمْ وَرَأَوُا۟ ٱلْعَذَابَ لَوْ أَنَّهُمْ كَانُوا۟ يَهْتَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa[1]!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ مَاذَآ أَجَبْتُمُ ٱلْمُرْسَلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: "Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَعَمِيَتْ عَلَيْهِمُ ٱلْأَنۢبَآءُ يَوْمَئِذٍ فَهُمْ لَا يَتَسَآءَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnansu ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَمَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحًا فَعَسَىٰٓ أَن يَكُونَ مِنَ ٱلْمُفْلِحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخْتَارُ مَا كَانَ لَهُمُ ٱلْخِيَرَةُ سُبْحَٰنَ ٱللَّهِ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَرَبُّكَ يَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَهُوَ ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ لَهُ ٱلْحَمْدُ فِى ٱلْأُولَىٰ وَٱلْـَٔاخِرَةِ وَلَهُ ٱلْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko (dũniya), da ta ƙarshe (Lãhira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمُ ٱلَّيْلَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَٰمَةِ مَنْ إِلَٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ يَأْتِيكُم بِضِيَآءٍ أَفَلَا تَسْمَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمُ ٱلنَّهَارَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَٰمَةِ مَنْ إِلَٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ يَأْتِيكُم بِلَيْلٍ تَسْكُنُونَ فِيهِ أَفَلَا تُبْصِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمِن رَّحْمَتِهِۦ جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ لِتَسْكُنُوا۟ فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, kuma tsammãninku zã ku gõde."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa"[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنَزَعْنَا مِن كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا فَقُلْنَا هَاتُوا۟ بُرْهَٰنَكُمْ فَعَلِمُوٓا۟ أَنَّ ٱلْحَقَّ لِلَّهِ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kãwo dalilinku." Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ قَٰرُونَ كَانَ مِن قَوْمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيْهِمْ وَءَاتَيْنَٰهُ مِنَ ٱلْكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلْعُصْبَةِ أُو۟لِى ٱلْقُوَّةِ إِذْ قَالَ لَهُۥ قَوْمُهُۥ لَا تَفْرَحْ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْفَرِحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita[1] daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a[2] ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱبْتَغِ فِيمَآ ءَاتَىٰكَ ٱللَّهُ ٱلدَّارَ ٱلْـَٔاخِرَةَ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ ٱلدُّنْيَا وَأَحْسِن كَمَآ أَحْسَنَ ٱللَّهُ إِلَيْكَ وَلَا تَبْغِ ٱلْفَسَادَ فِى ٱلْأَرْضِ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْمُفْسِدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa,[1] lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلْمٍ عِندِىٓ أَوَلَمْ يَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ قَدْ أَهْلَكَ مِن قَبْلِهِۦ مِنَ ٱلْقُرُونِ مَنْ هُوَ أَشَدُّ مِنْهُ قُوَّةً وَأَكْثَرُ جَمْعًا وَلَا يُسْـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلْمُجْرِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوْمِهِۦ فِى زِينَتِهِۦ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا يَٰلَيْتَ لَنَا مِثْلَ مَآ أُوتِىَ قَٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: "Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ وَيْلَكُمْ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيْرٌ لِّمَنْ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحًا وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّٰبِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai,[1] kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai haƙuri."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَخَسَفْنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلْأَرْضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٍ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلْمُنتَصِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Muka shãfe ƙasa[1] da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَصْبَحَ ٱلَّذِينَ تَمَنَّوْا۟ مَكَانَهُۥ بِٱلْأَمْسِ يَقُولُونَ وَيْكَأَنَّ ٱللَّهَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ وَيَقْدِرُ لَوْلَآ أَن مَّنَّ ٱللَّهُ عَلَيْنَا لَخَسَفَ بِنَا وَيْكَأَنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلْكَٰفِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, "Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تِلْكَ ٱلدَّارُ ٱلْـَٔاخِرَةُ نَجْعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوًّا فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فَسَادًا وَٱلْعَٰقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَن جَآءَ بِٱلْحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيْرٌ مِّنْهَا وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجْزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِى فَرَضَ عَلَيْكَ ٱلْقُرْءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٍ قُل رَّبِّىٓ أَعْلَمُ مَن جَآءَ بِٱلْهُدَىٰ وَمَنْ هُوَ فِى ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananne"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا كُنتَ تَرْجُوٓا۟ أَن يُلْقَىٰٓ إِلَيْكَ ٱلْكِتَٰبُ إِلَّا رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرًا لِّلْكَٰفِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako[1] ga kãfirai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا يَصُدُّنَّكَ عَنْ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بَعْدَ إِذْ أُنزِلَتْ إِلَيْكَ وَٱدْعُ إِلَىٰ رَبِّكَ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا تَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ كُلُّ شَىْءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجْهَهُۥ لَهُ ٱلْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskar Sa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70