وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدْيَنَ وَجَدَ عَلَيْهِ أُمَّةً مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسْقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمْرَأَتَيْنِ تَذُودَانِ قَالَ مَا خَطْبُكُمَا قَالَتَا لَا نَسْقِى حَتَّىٰ يُصْدِرَ ٱلرِّعَآءُ وَأَبُونَا شَيْخٌ كَبِيرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho[1] ne mai daraja."