caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Maa'un الماعون

Ayoyi 7 · Makka · tsarin saukarwa 17

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَذَٰلِكَ ٱلَّذِى يَدُعُّ ٱلْيَتِيمَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, wan nan shi ne ke tunkure marãya (daga haƙƙinsa).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَوَيْلٌ لِّلْمُصَلِّينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, bone yã tabbata ga masallata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗan da suke masu shagala daga sallar su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ هُمْ يُرَآءُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗan da suke yin riya (ga ayyukansu)

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَمْنَعُونَ ٱلْمَاعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suna hana taimako.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70