caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Hashr الحشر

Ayoyi 24 · Madina · tsarin saukarwa 101

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAbin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah, alhãli kuwa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هُوَ ٱلَّذِىٓ أَخْرَجَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَٰبِ مِن دِيَٰرِهِمْ لِأَوَّلِ ٱلْحَشْرِ مَا ظَنَنتُمْ أَن يَخْرُجُوا۟ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُم مَّانِعَتُهُمْ حُصُونُهُم مِّنَ ٱللَّهِ فَأَتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِنْ حَيْثُ لَمْ يَحْتَسِبُوا۟ وَقَذَفَ فِى قُلُوبِهِمُ ٱلرُّعْبَ يُخْرِبُونَ بُيُوتَهُم بِأَيْدِيهِمْ وَأَيْدِى ٱلْمُؤْمِنِينَ فَٱعْتَبِرُوا۟ يَٰٓأُو۟لِى ٱلْأَبْصَٰرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi,[1] daga gidãjẽnsu da kõra[2] ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْلَآ أَن كَتَبَ ٱللَّهُ عَلَيْهِمُ ٱلْجَلَآءَ لَعَذَّبَهُمْ فِى ٱلدُّنْيَا وَلَهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ عَذَابُ ٱلنَّارِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba dõmin Allah Ya rubuta musu kõrar ba, dã Ya azabta su a cikin dũniya, kuma a Lãhira sunã da azãbar wutã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ شَآقُّوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَمَن يُشَآقِّ ٱللَّهَ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWannan dõmin lalle su, sun sãɓa wa Allah, da ManzonSa alhãli kuwa wanda ya sãɓa wa Allah, to, lalle Allah, Mai tsananin uƙũba ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا قَطَعْتُم مِّن لِّينَةٍ أَوْ تَرَكْتُمُوهَا قَآئِمَةً عَلَىٰٓ أُصُولِهَا فَبِإِذْنِ ٱللَّهِ وَلِيُخْزِىَ ٱلْفَٰسِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAbin da kuka sãre na dabĩniya, kõ kuka bar ta tsaye a kan asallanta, to da iznin Allah ne, kuma dõmin Ya wulãkanta fasiƙai,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنْهُمْ فَمَآ أَوْجَفْتُمْ عَلَيْهِ مِنْ خَيْلٍ وَلَا رِكَابٍ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُسَلِّطُ رُسُلَهُۥ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga Manzon Sa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da Manzannin Sa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ مِنْ أَهْلِ ٱلْقُرَىٰ فَلِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِى ٱلْقُرْبَىٰ وَٱلْيَتَٰمَىٰ وَٱلْمَسَٰكِينِ وَٱبْنِ ٱلسَّبِيلِ كَىْ لَا يَكُونَ دُولَةًۢ بَيْنَ ٱلْأَغْنِيَآءِ مِنكُمْ وَمَآ ءَاتَىٰكُمُ ٱلرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَىٰكُمْ عَنْهُ فَٱنتَهُوا۟ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAbin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga Manzon Sa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na Manzon Sa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya[1] (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِلْفُقَرَآءِ ٱلْمُهَٰجِرِينَ ٱلَّذِينَ أُخْرِجُوا۟ مِن دِيَٰرِهِمْ وَأَمْوَٰلِهِمْ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضْوَٰنًا وَيَنصُرُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ أُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّٰدِقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da Manzon Sa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ تَبَوَّءُو ٱلدَّارَ وَٱلْإِيمَٰنَ مِن قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِى صُدُورِهِمْ حَاجَةً مِّمَّآ أُوتُوا۟ وَيُؤْثِرُونَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِۦ فَأُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu,[1] sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ جَآءُو مِنۢ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَٰنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلْإِيمَٰنِ وَلَا تَجْعَلْ فِى قُلُوبِنَا غِلًّا لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ رَبَّنَآ إِنَّكَ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نَافَقُوا۟ يَقُولُونَ لِإِخْوَٰنِهِمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَٰبِ لَئِنْ أُخْرِجْتُمْ لَنَخْرُجَنَّ مَعَكُمْ وَلَا نُطِيعُ فِيكُمْ أَحَدًا أَبَدًا وَإِن قُوتِلْتُمْ لَنَنصُرَنَّكُمْ وَٱللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّهُمْ لَكَٰذِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci[1]ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?" Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَئِنْ أُخْرِجُوا۟ لَا يَخْرُجُونَ مَعَهُمْ وَلَئِن قُوتِلُوا۟ لَا يَنصُرُونَهُمْ وَلَئِن نَّصَرُوهُمْ لَيُوَلُّنَّ ٱلْأَدْبَٰرَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan, zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَأَنتُمْ أَشَدُّ رَهْبَةً فِى صُدُورِهِم مِّنَ ٱللَّهِ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَفْقَهُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle kũ ne kuka fi bãyar da firgita a cikin zukãtansu bisa ga Allah, wannan kuwa dõmin sũ lalle waɗansu irin mutãne ne da bã su gãnẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا يُقَٰتِلُونَكُمْ جَمِيعًا إِلَّا فِى قُرًى مُّحَصَّنَةٍ أَوْ مِن وَرَآءِ جُدُرٍۭ بَأْسُهُم بَيْنَهُمْ شَدِيدٌ تَحْسَبُهُمْ جَمِيعًا وَقُلُوبُهُمْ شَتَّىٰ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَعْقِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã su iya yãƙar ku gabã ɗaya, fãce a cikin garũruwa mãsu gãnuwa da gãruna, kõ kuma daga bãyan katangu. Yãkinsu a tsãkaninsu mai tsanani ne, kanã zaton su a haɗe, alhãli kuwa zukãtansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle wasu irin mutane ne da bã su hankalta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَمَثَلِ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ قَرِيبًا ذَاقُوا۟ وَبَالَ أَمْرِهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar misãlin waɗanda[1] ke a gabãninsu, bã da daɗẽwa ba, sun ɗanɗani kũɗar al'amarinsu, kuma sunã da wata azãba mai radaɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَمَثَلِ ٱلشَّيْطَٰنِ إِذْ قَالَ لِلْإِنسَٰنِ ٱكْفُرْ فَلَمَّا كَفَرَ قَالَ إِنِّى بَرِىٓءٌ مِّنكَ إِنِّىٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلْعَٰلَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar misãlin Shaiɗan a lõkacin da yake cẽ wa mutum, "Ka kãfirta," To, a lõkacin da ya kãfirta ɗin, ya ce (masa): "Lalle bãbu ruwãna da kai. Lalle ni inã tsõron Allah Ubangijin halitta!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَكَانَ عَٰقِبَتَهُمَآ أَنَّهُمَا فِى ٱلنَّارِ خَٰلِدَيْنِ فِيهَا وَذَٰلِكَ جَزَٰٓؤُا۟ ٱلظَّٰلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, sunã mãsu dawwama a cikinta. "Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَلْتَنظُرْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ لِغَدٍ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا تَكُونُوا۟ كَٱلَّذِينَ نَسُوا۟ ٱللَّهَ فَأَنسَىٰهُمْ أَنفُسَهُمْ أُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلْفَٰسِقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rãyu, kansu. Waɗannan sũ ne fãsiƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا يَسْتَوِىٓ أَصْحَٰبُ ٱلنَّارِ وَأَصْحَٰبُ ٱلْجَنَّةِ أَصْحَٰبُ ٱلْجَنَّةِ هُمُ ٱلْفَآئِزُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYan Wutã da 'yan Aljanna bã su daidaita. 'Yan Aljanna, sũ ne mãsu babban rabo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَوْ أَنزَلْنَا هَٰذَا ٱلْقُرْءَانَ عَلَىٰ جَبَلٍ لَّرَأَيْتَهُۥ خَٰشِعًا مُّتَصَدِّعًا مِّنْ خَشْيَةِ ٱللَّهِ وَتِلْكَ ٱلْأَمْثَٰلُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِى لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ عَٰلِمُ ٱلْغَيْبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ هُوَ ٱلرَّحْمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِى لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلْمَلِكُ ٱلْقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلْمُؤْمِنُ ٱلْمُهَيْمِنُ ٱلْعَزِيزُ ٱلْجَبَّارُ ٱلْمُتَكَبِّرُ سُبْحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai tastãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هُوَ ٱللَّهُ ٱلْخَٰلِقُ ٱلْبَارِئُ ٱلْمُصَوِّرُ لَهُ ٱلْأَسْمَآءُ ٱلْحُسْنَىٰ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa. Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70