Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Alah ne zuwa gare ku?" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryama ya ce: "Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, Sũnansa Ahmad (Mashãyabo)." To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: "Wannan sihiri ne, bayyananne."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhãli kuwa shĩ, anã kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShi ne wanda Ya aiko Manzon Sa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu yi ĩmani da Allah da Manzon Sa, kuma ku yi jihãdi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wannan shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna da sani.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Allah Ya gãfarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗãkuna mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar zama. Wannan shĩ ne babban rabo, mai girma.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa wata (falala) da yake kunã son ta; taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushãra ga mũminai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga Hawãriyãwa, "Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu, sabõda haka suka wãyi gari marinjãya.