caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Saba سبإ

Ayoyi 54 · Makka · tsarin saukarwa 58

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِى لَهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ وَلَهُ ٱلْحَمْدُ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ وَهُوَ ٱلْحَكِيمُ ٱلْخَبِيرُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã Nãsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا وَهُوَ ٱلرَّحِيمُ ٱلْغَفُورُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai gãfara.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَا تَأْتِينَا ٱلسَّاعَةُ قُلْ بَلَىٰ وَرَبِّى لَتَأْتِيَنَّكُمْ عَٰلِمِ ٱلْغَيْبِ لَا يَعْزُبُ عَنْهُ مِثْقَالُ ذَرَّةٍ فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِى ٱلْأَرْضِ وَلَآ أَصْغَرُ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكْبَرُ إِلَّا فِى كِتَٰبٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi bayyananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِّيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ أُو۟لَٰٓئِكَ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ سَعَوْ فِىٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُو۟لَٰٓئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ مِّن رِّجْزٍ أَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi mãkirci ga ãyõyin Mu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗannan sunã da wata azãba daga azãba mai raɗaɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَرَى ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ هُوَ ٱلْحَقَّ وَيَهْدِىٓ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَمِيدِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi, Gõdadde.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ هَلْ نَدُلُّكُمْ عَلَىٰ رَجُلٍ يُنَبِّئُكُمْ إِذَا مُزِّقْتُمْ كُلَّ مُمَزَّقٍ إِنَّكُمْ لَفِى خَلْقٍ جَدِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفْتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَم بِهِۦ جِنَّةٌۢ بَلِ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ فِى ٱلْعَذَابِ وَٱلضَّلَٰلِ ٱلْبَعِيدِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ya ƙãga ƙarya ga Allah ne kõ kuwa akwai wata hauka a gare shi?" Ã'a, waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba, sunã a cikin azãba da ɓãta mai nĩsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَىٰ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ إِن نَّشَأْ نَخْسِفْ بِهِمُ ٱلْأَرْضَ أَوْ نُسْقِطْ عَلَيْهِمْ كِسَفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe fa, ba su yi dũbi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a bãyansu daga sama da ƙasã? idan Mun so, sai Mu shãfe ƙasã da su, kõ kuma Mu kãyar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai ãyã ga dukan bãwã mai maida al'amarinsa ga Allah.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا دَاوُۥدَ مِنَّا فَضْلًا يَٰجِبَالُ أَوِّبِى مَعَهُۥ وَٱلطَّيْرَ وَأَلَنَّا لَهُ ٱلْحَدِيدَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda wata falala dagagare Mu. Yã duwatsu, ku konkõma sautin tasbihi tãre da shi kuma da tsuntsãye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَنِ ٱعْمَلْ سَٰبِغَٰتٍ وَقَدِّرْ فِى ٱلسَّرْدِ وَٱعْمَلُوا۟ صَٰلِحًا إِنِّى بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa aikata sulkuna kuma ka ƙaddara lissãfi ga tsãrawa, kuma ka aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩ Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلِسُلَيْمَٰنَ ٱلرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهْرٌ وَرَوَاحُهَا شَهْرٌ وَأَسَلْنَا لَهُۥ عَيْنَ ٱلْقِطْرِ وَمِنَ ٱلْجِنِّ مَن يَعْمَلُ بَيْنَ يَدَيْهِ بِإِذْنِ رَبِّهِۦ وَمَن يَزِغْ مِنْهُمْ عَنْ أَمْرِنَا نُذِقْهُ مِنْ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ga Sulaimãn, Mun hõre masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudãnar masa da marmaron gaci, kuma daga aljannu (Muka hõre masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa. Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurnin Mu, sai Mu ɗanɗana masa daga azãbar sa'ĩr.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَعْمَلُونَ لَهُۥ مَا يَشَآءُ مِن مَّحَٰرِيبَ وَتَمَٰثِيلَ وَجِفَانٍ كَٱلْجَوَابِ وَقُدُورٍ رَّاسِيَٰتٍ ٱعْمَلُوٓا۟ ءَالَ دَاوُۥدَ شُكْرًا وَقَلِيلٌ مِّنْ عِبَادِىَ ٱلشَّكُورُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar kududdufai, da tukwãne kafaffu. Ku aikata gõdiya, yã ɗiyan Dãwũda, kuma kaɗan ne mai gõdiya daga bãyĩ Na.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّا قَضَيْنَا عَلَيْهِ ٱلْمَوْتَ مَا دَلَّهُمْ عَلَىٰ مَوْتِهِۦٓ إِلَّا دَآبَّةُ ٱلْأَرْضِ تَأْكُلُ مِنسَأَتَهُۥ فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ ٱلْجِنُّ أَن لَّوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ ٱلْغَيْبَ مَا لَبِثُوا۟ فِى ٱلْعَذَابِ ٱلْمُهِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan a lõkacin da Muka hukunta mutuwa a kansa bãbu abin da ya ja hankalinsu, a kan mutuwarsa, fãce dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To a lõkacin da ya fãɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutãne) cẽwa dã sun kasance sun san gaibi, dã ba su zauna ba a cikin azãba mai wulãkantarwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَقَدْ كَانَ لِسَبَإٍ فِى مَسْكَنِهِمْ ءَايَةٌ جَنَّتَانِ عَن يَمِينٍ وَشِمَالٍ كُلُوا۟ مِن رِّزْقِ رَبِّكُمْ وَٱشْكُرُوا۟ لَهُۥ بَلْدَةٌ طَيِّبَةٌ وَرَبٌّ غَفُورٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa[1] a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَعْرَضُوا۟ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ سَيْلَ ٱلْعَرِمِ وَبَدَّلْنَٰهُم بِجَنَّتَيْهِمْ جَنَّتَيْنِ ذَوَاتَىْ أُكُلٍ خَمْطٍ وَأَثْلٍ وَشَىْءٍ مِّن سِدْرٍ قَلِيلٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذَٰلِكَ جَزَيْنَٰهُم بِمَا كَفَرُوا۟ وَهَلْ نُجَٰزِىٓ إِلَّا ٱلْكَفُورَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa[1] irin wannan sakamako, fãce kafirai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ ٱلْقُرَى ٱلَّتِى بَٰرَكْنَا فِيهَا قُرًى ظَٰهِرَةً وَقَدَّرْنَا فِيهَا ٱلسَّيْرَ سِيرُوا۟ فِيهَا لَيَالِىَ وَأَيَّامًا ءَامِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin[1] garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَقَالُوا۟ رَبَّنَا بَٰعِدْ بَيْنَ أَسْفَارِنَا وَظَلَمُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ فَجَعَلْنَٰهُمْ أَحَادِيثَ وَمَزَّقْنَٰهُمْ كُلَّ مُمَزَّقٍ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَٰتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce[1] su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ صَدَّقَ عَلَيْهِمْ إِبْلِيسُ ظَنَّهُۥ فَٱتَّبَعُوهُ إِلَّا فَرِيقًا مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi fãce wani ɓangare na mũminai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا كَانَ لَهُۥ عَلَيْهِم مِّن سُلْطَٰنٍ إِلَّا لِنَعْلَمَ مَن يُؤْمِنُ بِٱلْـَٔاخِرَةِ مِمَّنْ هُوَ مِنْهَا فِى شَكٍّ وَرَبُّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ حَفِيظٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلِ ٱدْعُوا۟ ٱلَّذِينَ زَعَمْتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمْلِكُونَ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا لَهُمْ فِيهِمَا مِن شِرْكٍ وَمَا لَهُۥ مِنْهُم مِّن ظَهِيرٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ عِندَهُۥٓ إِلَّا لِمَنْ أَذِنَ لَهُۥ حَتَّىٰٓ إِذَا فُزِّعَ عَن قُلُوبِهِمْ قَالُوا۟ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ قَالُوا۟ ٱلْحَقَّ وَهُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْكَبِيرُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurin Sa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye[1] tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ قُلِ ٱللَّهُ وَإِنَّآ أَوْ إِيَّاكُمْ لَعَلَىٰ هُدًى أَوْ فِى ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُل لَّا تُسْـَٔلُونَ عَمَّآ أَجْرَمْنَا وَلَا نُسْـَٔلُ عَمَّا تَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ يَجْمَعُ بَيْنَنَا رَبُّنَا ثُمَّ يَفْتَحُ بَيْنَنَا بِٱلْحَقِّ وَهُوَ ٱلْفَتَّاحُ ٱلْعَلِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَرُونِىَ ٱلَّذِينَ أَلْحَقْتُم بِهِۦ شُرَكَآءَ كَلَّا بَلْ هُوَ ٱللَّهُ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَرْسَلْنَٰكَ إِلَّا كَآفَّةً لِّلنَّاسِ بَشِيرًا وَنَذِيرًا وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُل لَّكُم مِّيعَادُ يَوْمٍ لَّا تَسْتَـْٔخِرُونَ عَنْهُ سَاعَةً وَلَا تَسْتَقْدِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَن نُّؤْمِنَ بِهَٰذَا ٱلْقُرْءَانِ وَلَا بِٱلَّذِى بَيْنَ يَدَيْهِ وَلَوْ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّٰلِمُونَ مَوْقُوفُونَ عِندَ رَبِّهِمْ يَرْجِعُ بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ ٱلْقَوْلَ يَقُولُ ٱلَّذِينَ ٱسْتُضْعِفُوا۟ لِلَّذِينَ ٱسْتَكْبَرُوا۟ لَوْلَآ أَنتُمْ لَكُنَّا مُؤْمِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ ٱلَّذِينَ ٱسْتَكْبَرُوا۟ لِلَّذِينَ ٱسْتُضْعِفُوٓا۟ أَنَحْنُ صَدَدْنَٰكُمْ عَنِ ٱلْهُدَىٰ بَعْدَ إِذْ جَآءَكُم بَلْ كُنتُم مُّجْرِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMakangara suka ce wa maraunana, "Ashe, mũ ne muka kange ku daga shiriya a bãyan ya zo muku? Ã, a' kun dai kasance mãsu laifi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱسْتُضْعِفُوا۟ لِلَّذِينَ ٱسْتَكْبَرُوا۟ بَلْ مَكْرُ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ إِذْ تَأْمُرُونَنَآ أَن نَّكْفُرَ بِٱللَّهِ وَنَجْعَلَ لَهُۥٓ أَندَادًا وَأَسَرُّوا۟ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُا۟ ٱلْعَذَابَ وَجَعَلْنَا ٱلْأَغْلَٰلَ فِىٓ أَعْنَاقِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma maraunana suka ce wa makangara. "Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya." Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَرْسَلْنَا فِى قَرْيَةٍ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَآ إِنَّا بِمَآ أُرْسِلْتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya fãce mani'imtanta (shũgabanni) sunce, "Lalle mũ, mãsu kãfirta ne da abin da aka aiko ku da shi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالُوا۟ نَحْنُ أَكْثَرُ أَمْوَٰلًا وَأَوْلَٰدًا وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce: "Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ إِنَّ رَبِّى يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقْدِرُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfiɗa arziki ga wanda Ya so, kuma Yanã ƙuntatãwa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَمْوَٰلُكُمْ وَلَآ أَوْلَٰدُكُم بِٱلَّتِى تُقَرِّبُكُمْ عِندَنَا زُلْفَىٰٓ إِلَّا مَنْ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحًا فَأُو۟لَٰٓئِكَ لَهُمْ جَزَآءُ ٱلضِّعْفِ بِمَا عَمِلُوا۟ وَهُمْ فِى ٱلْغُرُفَٰتِ ءَامِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnãye.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ يَسْعَوْنَ فِىٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُو۟لَٰٓئِكَ فِى ٱلْعَذَابِ مُحْضَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suke mãkirci a cikin ãyõyinMu, sunã nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartãwa ne a cikin azãba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ إِنَّ رَبِّى يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ وَيَقْدِرُ لَهُۥ وَمَآ أَنفَقْتُم مِّن شَىْءٍ فَهُوَ يُخْلِفُهُۥ وَهُوَ خَيْرُ ٱلرَّٰزِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَوْمَ يَحْشُرُهُمْ جَمِيعًا ثُمَّ يَقُولُ لِلْمَلَٰٓئِكَةِ أَهَٰٓؤُلَآءِ إِيَّاكُمْ كَانُوا۟ يَعْبُدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, "Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ سُبْحَٰنَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِم بَلْ كَانُوا۟ يَعْبُدُونَ ٱلْجِنَّ أَكْثَرُهُم بِهِم مُّؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSukace: "Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bã su ba. Ã'a, sun kasance sunã bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلْيَوْمَ لَا يَمْلِكُ بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ نَّفْعًا وَلَا ضَرًّا وَنَقُولُ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ذُوقُوا۟ عَذَابَ ٱلنَّارِ ٱلَّتِى كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda "kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٍ قَالُوا۟ مَا هَٰذَآ إِلَّا رَجُلٌ يُرِيدُ أَن يَصُدَّكُمْ عَمَّا كَانَ يَعْبُدُ ءَابَآؤُكُمْ وَقَالُوا۟ مَا هَٰذَآ إِلَّآ إِفْكٌ مُّفْتَرًى وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِلْحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمْ إِنْ هَٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan an karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga." Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: "Wannan bã kõme ba fãce sihiri ne bayyananne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ ءَاتَيْنَٰهُم مِّن كُتُبٍ يَدْرُسُونَهَا وَمَآ أَرْسَلْنَآ إِلَيْهِمْ قَبْلَكَ مِن نَّذِيرٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu bã su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karãtun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabãninka!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَمَا بَلَغُوا۟ مِعْشَارَ مَآ ءَاتَيْنَٰهُمْ فَكَذَّبُوا۟ رُسُلِى فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata, alhãli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata Manzanni Na! To, yãya musũ Na (ga maƙaryata) ya kasance?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ إِنَّمَآ أَعِظُكُم بِوَٰحِدَةٍ أَن تَقُومُوا۟ لِلَّهِ مَثْنَىٰ وَفُرَٰدَىٰ ثُمَّ تَتَفَكَّرُوا۟ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍ إِنْ هُوَ إِلَّا نَذِيرٌ لَّكُم بَيْنَ يَدَىْ عَذَابٍ شَدِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ مَا سَأَلْتُكُم مِّنْ أَجْرٍ فَهُوَ لَكُمْ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Abin da na rõƙe ku na wani sakamako, to, amfãninsa nãku ne. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma shi Ma shadai ne a kan dukan kõme."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ إِنَّ رَبِّى يَقْذِفُ بِٱلْحَقِّ عَلَّٰمُ ٱلْغُيُوبِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Lalle Ubangijina Yanã jẽfa gaskiya. (Shi) Masanin abũbuwan fake ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ جَآءَ ٱلْحَقُّ وَمَا يُبْدِئُ ٱلْبَٰطِلُ وَمَا يُعِيدُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bã ta iya fara (kome) kuma bã ta iya mayarwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ إِن ضَلَلْتُ فَإِنَّمَآ أَضِلُّ عَلَىٰ نَفْسِى وَإِنِ ٱهْتَدَيْتُ فَبِمَا يُوحِىٓ إِلَىَّ رَبِّىٓ إِنَّهُۥ سَمِيعٌ قَرِيبٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ تَرَىٰٓ إِذْ فَزِعُوا۟ فَلَا فَوْتَ وَأُخِذُوا۟ مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dã kã gani, a lõkacin da suka firgita, to, bãbu kuɓuta, kuma aka kãma su daga wuri makusanci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِهِۦ وَأَنَّىٰ لَهُمُ ٱلتَّنَاوُشُ مِن مَّكَانٍۭ بَعِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce: "Mun yi ĩmãni da Shi." To inã zã su sãmu kãmãwa daga wuri mai nisa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَدْ كَفَرُوا۟ بِهِۦ مِن قَبْلُ وَيَقْذِفُونَ بِٱلْغَيْبِ مِن مَّكَانٍۭ بَعِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle sun kãfirta da Shi a gabãnin haka, kuma sunã jĩfa da jãhilci daga wuri mai nĩsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَحِيلَ بَيْنَهُمْ وَبَيْنَ مَا يَشْتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشْيَاعِهِم مِّن قَبْلُ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ فِى شَكٍّ مُّرِيبٍۭ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kõkanto.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70