قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ قُلِ ٱللَّهُ وَإِنَّآ أَوْ إِيَّاكُمْ لَعَلَىٰ هُدًى أَوْ فِى ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya."