caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Baqara, aya 235

Madina · tsarin saukarwa 87 · 2:235

وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا عَرَّضْتُم بِهِۦ مِنْ خِطْبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوْ أَكْنَنتُمْ فِىٓ أَنفُسِكُمْ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمْ سَتَذْكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُوا۟ قَوْلًا مَّعْرُوفًا وَلَا تَعْزِمُوا۟ عُقْدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبْلُغَ ٱلْكِتَٰبُ أَجَلَهُۥ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِىٓ أَنفُسِكُمْ فَٱحْذَرُوهُ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta[1] da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70