caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu At-Tawba, aya 120

Madina · tsarin saukarwa 113 · 9:120

مَا كَانَ لِأَهْلِ ٱلْمَدِينَةِ وَمَنْ حَوْلَهُم مِّنَ ٱلْأَعْرَابِ أَن يَتَخَلَّفُوا۟ عَن رَّسُولِ ٱللَّهِ وَلَا يَرْغَبُوا۟ بِأَنفُسِهِمْ عَن نَّفْسِهِۦ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ لَا يُصِيبُهُمْ ظَمَأٌ وَلَا نَصَبٌ وَلَا مَخْمَصَةٌ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَطَـُٔونَ مَوْطِئًا يَغِيظُ ٱلْكُفَّارَ وَلَا يَنَالُونَ مِنْ عَدُوٍّ نَّيْلًا إِلَّا كُتِبَ لَهُم بِهِۦ عَمَلٌ صَٰلِحٌ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجْرَ ٱلْمُحْسِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã ya kasancẽwa[1] ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70