caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu At-Talaaq, aya 1

Madina · tsarin saukarwa 99 · 65:1

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِىُّ إِذَا طَلَّقْتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحْصُوا۟ ٱلْعِدَّةَ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ رَبَّكُمْ لَا تُخْرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخْرُجْنَ إِلَّآ أَن يَأْتِينَ بِفَٰحِشَةٍ مُّبَيِّنَةٍ وَتِلْكَ حُدُودُ ٱللَّهِ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدْ ظَلَمَ نَفْسَهُۥ لَا تَدْرِى لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحْدِثُ بَعْدَ ذَٰلِكَ أَمْرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu,[1] kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70