caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-A'raaf, aya 38

Makka · tsarin saukarwa 39 · 7:38

قَالَ ٱدْخُلُوا۟ فِىٓ أُمَمٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِكُم مِّنَ ٱلْجِنِّ وَٱلْإِنسِ فِى ٱلنَّارِ كُلَّمَا دَخَلَتْ أُمَّةٌ لَّعَنَتْ أُخْتَهَا حَتَّىٰٓ إِذَا ٱدَّارَكُوا۟ فِيهَا جَمِيعًا قَالَتْ أُخْرَىٰهُمْ لِأُولَىٰهُمْ رَبَّنَا هَٰٓؤُلَآءِ أَضَلُّونَا فَـَٔاتِهِمْ عَذَابًا ضِعْفًا مِّنَ ٱلنَّارِ قَالَ لِكُلٍّ ضِعْفٌ وَلَٰكِن لَّا تَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane[1] akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70