caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-A'raaf, aya 37

Makka · tsarin saukarwa 39 · 7:37

فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ ٱفْتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓ أُو۟لَٰٓئِكَ يَنَالُهُمْ نَصِيبُهُم مِّنَ ٱلْكِتَٰبِ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَتْهُمْ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوْنَهُمْ قَالُوٓا۟ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ قَالُوا۟ ضَلُّوا۟ عَنَّا وَشَهِدُوا۟ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ أَنَّهُمْ كَانُوا۟ كَٰفِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70