يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ شَهَٰدَةُ بَيْنِكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلْمَوْتُ حِينَ ٱلْوَصِيَّةِ ٱثْنَانِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ أَوْ ءَاخَرَانِ مِنْ غَيْرِكُمْ إِنْ أَنتُمْ ضَرَبْتُمْ فِى ٱلْأَرْضِ فَأَصَٰبَتْكُم مُّصِيبَةُ ٱلْمَوْتِ تَحْبِسُونَهُمَا مِنۢ بَعْدِ ٱلصَّلَوٰةِ فَيُقْسِمَانِ بِٱللَّهِ إِنِ ٱرْتَبْتُمْ لَا نَشْتَرِى بِهِۦ ثَمَنًا وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَىٰ وَلَا نَكْتُمُ شَهَٰدَةَ ٱللَّهِ إِنَّآ إِذًا لَّمِنَ ٱلْـَٔاثِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar[1] tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfar mutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi."