caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Baqara, aya 259

Madina · tsarin saukarwa 87 · 2:259

أَوْ كَٱلَّذِى مَرَّ عَلَىٰ قَرْيَةٍ وَهِىَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحْىِۦ هَٰذِهِ ٱللَّهُ بَعْدَ مَوْتِهَا فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِا۟ئَةَ عَامٍ ثُمَّ بَعَثَهُۥ قَالَ كَمْ لَبِثْتَ قَالَ لَبِثْتُ يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ قَالَ بَل لَّبِثْتَ مِا۟ئَةَ عَامٍ فَٱنظُرْ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمْ يَتَسَنَّهْ وَٱنظُرْ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجْعَلَكَ ءَايَةً لِّلنَّاسِ وَٱنظُرْ إِلَى ٱلْعِظَامِ كَيْفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكْسُوهَا لَحْمًا فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعْلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKõ kuwa[1] wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70