caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu An-Nisaa, aya 88

Madina · tsarin saukarwa 92 · 4:88

فَمَا لَكُمْ فِى ٱلْمُنَٰفِقِينَ فِئَتَيْنِ وَٱللَّهُ أَرْكَسَهُم بِمَا كَسَبُوٓا۟ أَتُرِيدُونَ أَن تَهْدُوا۟ مَنْ أَضَلَّ ٱللَّهُ وَمَن يُضْلِلِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ سَبِيلًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, mẽne ne ya sãme[1] ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70