قُلْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنِّى رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ فَـَٔامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِ ٱلنَّبِىِّ ٱلْأُمِّىِّ ٱلَّذِى يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَكَلِمَٰتِهِۦ وَٱتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Yã kũ mutãne![1] Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."