وَإِذَا جَآءَتْهُمْ ءَايَةٌ قَالُوا۟ لَن نُّؤْمِنَ حَتَّىٰ نُؤْتَىٰ مِثْلَ مَآ أُوتِىَ رُسُلُ ٱللَّهِ ٱللَّهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسَالَتَهُۥ سَيُصِيبُ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ صَغَارٌ عِندَ ٱللَّهِ وَعَذَابٌ شَدِيدٌۢ بِمَا كَانُوا۟ يَمْكُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa.[1] Wani wulaƙanci[2] a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.