caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Baqara, aya 253

Madina · tsarin saukarwa 87 · 2:253

تِلْكَ ٱلرُّسُلُ فَضَّلْنَا بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ مِّنْهُم مَّن كَلَّمَ ٱللَّهُ وَرَفَعَ بَعْضَهُمْ دَرَجَٰتٍ وَءَاتَيْنَا عِيسَى ٱبْنَ مَرْيَمَ ٱلْبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدْنَٰهُ بِرُوحِ ٱلْقُدُسِ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقْتَتَلَ ٱلَّذِينَ مِنۢ بَعْدِهِم مِّنۢ بَعْدِ مَا جَآءَتْهُمُ ٱلْبَيِّنَٰتُ وَلَٰكِنِ ٱخْتَلَفُوا۟ فَمِنْهُم مَّنْ ءَامَنَ وَمِنْهُم مَّن كَفَرَ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقْتَتَلُوا۟ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَفْعَلُ مَا يُرِيدُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗancan manzannin[1] Mun fĩfĩta sãshensu a kan sãshe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sãshensu da darajõji; kuma Muka bai wa Ĩsã dan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafã shi da Rũhi mai tsarki. Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70