caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Baqara, aya 126

Madina · tsarin saukarwa 87 · 2:126

وَإِذْ قَالَ إِبْرَٰهِـۧمُ رَبِّ ٱجْعَلْ هَٰذَا بَلَدًا ءَامِنًا وَٱرْزُقْ أَهْلَهُۥ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ مَنْ ءَامَنَ مِنْهُم بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ قَالَ وَمَن كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُۥ قَلِيلًا ثُمَّ أَضْطَرُّهُۥٓ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلنَّارِ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira." Allah Ya ce: "Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70