caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu At-Tawba, aya 107

Madina · tsarin saukarwa 113 · 9:107

وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُوا۟ مَسْجِدًا ضِرَارًا وَكُفْرًا وَتَفْرِيقًۢا بَيْنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَإِرْصَادًا لِّمَنْ حَارَبَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ مِن قَبْلُ وَلَيَحْلِفُنَّ إِنْ أَرَدْنَآ إِلَّا ٱلْحُسْنَىٰ وَٱللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّهُمْ لَكَٰذِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda[1] suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70