caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu An-Nisaa, aya 135

Madina · tsarin saukarwa 92 · 4:135

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُونُوا۟ قَوَّٰمِينَ بِٱلْقِسْطِ شُهَدَآءَ لِلَّهِ وَلَوْ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمْ أَوِ ٱلْوَٰلِدَيْنِ وَٱلْأَقْرَبِينَ إِن يَكُنْ غَنِيًّا أَوْ فَقِيرًا فَٱللَّهُ أَوْلَىٰ بِهِمَا فَلَا تَتَّبِعُوا۟ ٱلْهَوَىٰٓ أَن تَعْدِلُوا۟ وَإِن تَلْوُۥٓا۟ أَوْ تُعْرِضُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida[1] sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70