إِذْ قَالَتِ ٱلْمَلَٰٓئِكَةُ يَٰمَرْيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَةٍ مِّنْهُ ٱسْمُهُ ٱلْمَسِيحُ عِيسَى ٱبْنُ مَرْيَمَ وَجِيهًا فِى ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةِ وَمِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta.