ذَٰلِكَ مِنْ أَنۢبَآءِ ٱلْغَيْبِ نُوحِيهِ إِلَيْكَ وَمَا كُنتَ لَدَيْهِمْ إِذْ يُلْقُونَ أَقْلَٰمَهُمْ أَيُّهُمْ يَكْفُلُ مَرْيَمَ وَمَا كُنتَ لَدَيْهِمْ إِذْ يَخْتَصِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWannan yana daga lãbarun[1] gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma[2].