وَلَتَجِدَنَّهُمْ أَحْرَصَ ٱلنَّاسِ عَلَىٰ حَيَوٰةٍ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ يَوَدُّ أَحَدُهُمْ لَوْ يُعَمَّرُ أَلْفَ سَنَةٍ وَمَا هُوَ بِمُزَحْزِحِهِۦ مِنَ ٱلْعَذَابِ أَن يُعَمَّرَ وَٱللَّهُ بَصِيرٌۢ بِمَا يَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son dã zã a rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.