وَإِن تَعْجَبْ فَعَجَبٌ قَوْلُهُمْ أَءِذَا كُنَّا تُرَٰبًا أَءِنَّا لَفِى خَلْقٍ جَدِيدٍ أُو۟لَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِرَبِّهِمْ وَأُو۟لَٰٓئِكَ ٱلْأَغْلَٰلُ فِىٓ أَعْنَاقِهِمْ وَأُو۟لَٰٓئِكَ أَصْحَٰبُ ٱلنَّارِ هُمْ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan ka yi mãmãki, to, mãmãkin kam shi ne maganarsu, "Shin, idan muka kasance turɓãya, zã mu zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, kuma waɗanda akwai ƙuƙumai a cikin wuyõyinsu, kuma waɗancan ne abõkan wuta. Sũ, a cikinta, mãsu dawwama ne.