وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبْلَ ٱلْحَسَنَةِ وَقَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِمُ ٱلْمَثُلَٰتُ وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغْفِرَةٍ لِّلنَّاسِ عَلَىٰ ظُلْمِهِمْ وَإِنَّ رَبَّكَ لَشَدِيدُ ٱلْعِقَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sunã nẽman ka da gaggãwa da azãba a gabãnin rahama, alhãli kuwa abũbuwan misãli sun gabãta a gabãninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne ga mutãne a kan zãluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai tsananin uƙũba ne.