caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Ghaafir, aya 7

Makka · tsarin saukarwa 60 · 40:7

ٱلَّذِينَ يَحْمِلُونَ ٱلْعَرْشَ وَمَنْ حَوْلَهُۥ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَيُؤْمِنُونَ بِهِۦ وَيَسْتَغْفِرُونَ لِلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ رَبَّنَا وَسِعْتَ كُلَّ شَىْءٍ رَّحْمَةً وَعِلْمًا فَٱغْفِرْ لِلَّذِينَ تَابُوا۟ وَٱتَّبَعُوا۟ سَبِيلَكَ وَقِهِمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70