وَمَا كَانَ لِنَبِىٍّ أَن يَغُلَّ وَمَن يَغْلُلْ يَأْتِ بِمَا غَلَّ يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu.[1] Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba.