caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Baqara, aya 232

Madina · tsarin saukarwa 87 · 2:232

وَإِذَا طَلَّقْتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا تَعْضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحْنَ أَزْوَٰجَهُنَّ إِذَا تَرَٰضَوْا۟ بَيْنَهُم بِٱلْمَعْرُوفِ ذَٰلِكَ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ مِنكُمْ يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ ذَٰلِكُمْ أَزْكَىٰ لَكُمْ وَأَطْهَرُ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70