caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Baqara, aya 136

Madina · tsarin saukarwa 87 · 2:136

قُولُوٓا۟ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَآ أُنزِلَ إِلَىٰٓ إِبْرَٰهِـۧمَ وَإِسْمَٰعِيلَ وَإِسْحَٰقَ وَيَعْقُوبَ وَٱلْأَسْبَاطِ وَمَآ أُوتِىَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَمَآ أُوتِىَ ٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمْ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّنْهُمْ وَنَحْنُ لَهُۥ مُسْلِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu[1] ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne."
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70