caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Baqara, aya 113

Madina · tsarin saukarwa 87 · 2:113

وَقَالَتِ ٱلْيَهُودُ لَيْسَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ عَلَىٰ شَىْءٍ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَىٰ لَيْسَتِ ٱلْيَهُودُ عَلَىٰ شَىْءٍ وَهُمْ يَتْلُونَ ٱلْكِتَٰبَ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ مِثْلَ قَوْلِهِمْ فَٱللَّهُ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba,"[1] kuma Nasãra suka ce: "Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70