إِنَّمَا ٱلصَّدَقَٰتُ لِلْفُقَرَآءِ وَٱلْمَسَٰكِينِ وَٱلْعَٰمِلِينَ عَلَيْهَا وَٱلْمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِى ٱلرِّقَابِ وَٱلْغَٰرِمِينَ وَفِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱبْنِ ٱلسَّبِيلِ فَرِيضَةً مِّنَ ٱللَّهِ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAbin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.