بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْأَنفَالِ قُلِ ٱلْأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِ فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَصْلِحُوا۟ ذَاتَ بَيْنِكُمْ وَأَطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuna tambayar ka[1] ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance Mũminai."