فَقَدْ كَذَّبُوا۟ بِٱلْحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمْ فَسَوْفَ يَأْتِيهِمْ أَنۢبَٰٓؤُا۟ مَا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu.