caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu An-Nisaa, aya 173

Madina · tsarin saukarwa 92 · 4:173

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضْلِهِۦ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ٱسْتَنكَفُوا۟ وَٱسْتَكْبَرُوا۟ فَيُعَذِّبُهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا وَلَا يَجِدُونَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to zã Ya cika musu ijãrõrinsu, kuma Yanã ƙãra musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyãma, kuma suka yi girman kai, to, zã Ya yi musu azãba, azãba mai raɗɗi kuma bã su samun wani masõyi dõmin kansu, baicin Allah, kuma bã su samun mataimaki.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70