caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Ahzaab, aya 53

Madina · tsarin saukarwa 90 · 33:53

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَدْخُلُوا۟ بُيُوتَ ٱلنَّبِىِّ إِلَّآ أَن يُؤْذَنَ لَكُمْ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيْرَ نَٰظِرِينَ إِنَىٰهُ وَلَٰكِنْ إِذَا دُعِيتُمْ فَٱدْخُلُوا۟ فَإِذَا طَعِمْتُمْ فَٱنتَشِرُوا۟ وَلَا مُسْتَـْٔنِسِينَ لِحَدِيثٍ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ يُؤْذِى ٱلنَّبِىَّ فَيَسْتَحْىِۦ مِنكُمْ وَٱللَّهُ لَا يَسْتَحْىِۦ مِنَ ٱلْحَقِّ وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَٰعًا فَسْـَٔلُوهُنَّ مِن وَرَآءِ حِجَابٍ ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ وَمَا كَانَ لَكُمْ أَن تُؤْذُوا۟ رَسُولَ ٱللَّهِ وَلَآ أَن تَنكِحُوٓا۟ أَزْوَٰجَهُۥ مِنۢ بَعْدِهِۦٓ أَبَدًا إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70