ٱدْعُوهُمْ لِـَٔابَآئِهِمْ هُوَ أَقْسَطُ عِندَ ٱللَّهِ فَإِن لَّمْ تَعْلَمُوٓا۟ ءَابَآءَهُمْ فَإِخْوَٰنُكُمْ فِى ٱلدِّينِ وَمَوَٰلِيكُمْ وَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ فِيمَآ أَخْطَأْتُم بِهِۦ وَلَٰكِن مَّا تَعَمَّدَتْ قُلُوبُكُمْ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.