caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Ahzaab, aya 33

Madina · tsarin saukarwa 90 · 33:33

وَقَرْنَ فِى بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ ٱلْجَٰهِلِيَّةِ ٱلْأُولَىٰ وَأَقِمْنَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتِينَ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِعْنَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنكُمُ ٱلرِّجْسَ أَهْلَ ٱلْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ku tabbata a cikin gidãjenku,[1] kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã, ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70