لَّا يَتَّخِذِ ٱلْمُؤْمِنُونَ ٱلْكَٰفِرِينَ أَوْلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ فَلَيْسَ مِنَ ٱللَّهِ فِى شَىْءٍ إِلَّآ أَن تَتَّقُوا۟ مِنْهُمْ تُقَىٰةً وَيُحَذِّرُكُمُ ٱللَّهُ نَفْسَهُۥ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلْمَصِيرُ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma take.