caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Aal-i-Imraan, aya 195

Madina · tsarin saukarwa 89 · 3:195

فَٱسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّى لَآ أُضِيعُ عَمَلَ عَٰمِلٍ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ بَعْضُكُم مِّنۢ بَعْضٍ فَٱلَّذِينَ هَاجَرُوا۟ وَأُخْرِجُوا۟ مِن دِيَٰرِهِمْ وَأُوذُوا۟ فِى سَبِيلِى وَقَٰتَلُوا۟ وَقُتِلُوا۟ لَأُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّـَٔاتِهِمْ وَلَأُدْخِلَنَّهُمْ جَنَّٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَٰرُ ثَوَابًا مِّنْ عِندِ ٱللَّهِ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسْنُ ٱلثَّوَابِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako.
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70