لَّقَدْ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوْلَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ فَقِيرٌ وَنَحْنُ أَغْنِيَآءُ سَنَكْتُبُ مَا قَالُوا۟ وَقَتْلَهُمُ ٱلْأَنۢبِيَآءَ بِغَيْرِ حَقٍّ وَنَقُولُ ذُوقُوا۟ عَذَابَ ٱلْحَرِيقِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: "Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu." za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: "Ku ɗanɗani azãbar gõbara!