وَلَا يَحْزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَٰرِعُونَ فِى ٱلْكُفْرِ إِنَّهُمْ لَن يَضُرُّوا۟ ٱللَّهَ شَيْـًٔا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَلَّا يَجْعَلَ لَهُمْ حَظًّا فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma.