فَإِذَا قَضَيْتُم مَّنَٰسِكَكُمْ فَٱذْكُرُوا۟ ٱللَّهَ كَذِكْرِكُمْ ءَابَآءَكُمْ أَوْ أَشَدَّ ذِكْرًا فَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِى ٱلدُّنْيَا وَمَا لَهُۥ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ مِنْ خَلَٰقٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan kun ƙãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: "Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wanirabo a cikin Lãhira.