رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا فَٱعْبُدْهُ وَٱصْطَبِرْ لِعِبَٰدَتِهِۦ هَلْ تَعْلَمُ لَهُۥ سَمِيًّا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãnin su. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautar sa. Shin kã san wani takwara a gare shi?