وَجَآءَتْ سَيَّارَةٌ فَأَرْسَلُوا۟ وَارِدَهُمْ فَأَدْلَىٰ دَلْوَهُۥ قَالَ يَٰبُشْرَىٰ هَٰذَا غُلَٰمٌ وَأَسَرُّوهُ بِضَٰعَةً وَٱللَّهُ عَلِيمٌۢ بِمَا يَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wani ãyari[1] ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.