يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَا لَكُمْ إِذَا قِيلَ لَكُمُ ٱنفِرُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱثَّاقَلْتُمْ إِلَى ٱلْأَرْضِ أَرَضِيتُم بِٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا مِنَ ٱلْـَٔاخِرَةِ فَمَا مَتَٰعُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ إِلَّا قَلِيلٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi[1] zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan.